Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya yabawa hamshakin attajirin Afrika Aliko Dangote bisa sadaukar da kashi 25 na dukiyarsa ga ayyukan agaji.
Ya bayyana hakan ne a matsayin wani mataki mai kawo sauyi ga ci gaban kasa da kuma abin koyi ga ayyukan jin kai a fadin Afirka.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin wani babban taro da aka gudanar a Legas wanda ya samu halartar mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, gwamnonin jihohin Kano da na Gombe da Nasarawa da Borno da kuma ministocin ilimi.
A wajen taron Gidauniyar Aliko Dangote ta kaddamar da shirin tallafawa ilimi na Naira biliyan 100 wanda ya shafi dalibai 155,000 a fadin kasar.

Gidauniyar ta kuma sanar da wani shiri na dogon lokaci na zuba jarin da ya kai Naira tiriliyan 1 a cikin shekaru goma masu zuwa domin kaiwa sama da mutane miliyan 1.3 da za su ci gajiyar tallafin tare da mai da hankali sosai kan yaran da ba su zuwa makaranta.
Gwamna Yusuf ya lura da cewa shirin ya yi daidai da kokarin kasa baki daya na inganta hanyoyin samun dama ingancin malamai da ababen more rayuwa na ilmantarwa wanda ke karfafa sauye-sauyen ilimi da Kano ke ci gaba da yi a karkashin dokar ta baci da jihar ta ayyana a fannin.
Ya bayyana cigaban da aka samu a Kano a baya-bayan nan, da suka hada da daukar malamai sama da 13,000 da gyara manyan makarantu da rage cunkoson ajujuwa da rarraba tebura da kuma fadada tallafin karatu.
Har ila yau jihar na gudanar da bincike don gano yaran da ba su zuwa makaranta da kuma shigar da makarantun kur’ani a cikin ilimi na yau da kullum.
Ya kuma yi maraba da matakin da Gidauniyar ta dauka na zuba jarin Naira biliyan 15 wajen inganta Jami’ar Aliko Dangote da ke Wudil zuwa matsayin kasa da kasa, yana mai cewa hakan zai kara inganta ilimin manyan makarantu da samun dama ga Kano da ma kasa baki daya.
Gwamna Yusuf ya sake jaddada aniyar Kano na tabbatar da cewa kowane yaro dan Najeriya ya samu ilimin aiki sannan ya ce hadin gwiwa da cibiyoyi irin su gidauniyar Dangote na da matukar muhimmanci wajen cimma wannan buri.
Ya bayyana kwarin gwiwar cewa, hadin gwiwar za ta samar da fa’ida ta dogon lokaci da kuma kara kaimi wajen dakile gibin koyo a fadin kasar nan.