Take a fresh look at your lifestyle.

Gwamnan Akwa Ibom Ya Nanata Alkawarin Ci GabaDa Zaman Lafiya 

75

Gwamnan Jihar Akwa Ibom Fasto Umo Eno ya ja hankalin al’ummar jihar cikin sabuwar shekara tare da jaddada kudirin gwamnatinsa na samar da zaman lafiya da ci gaban kasa da kuma tsarin kasafin kudi.

A jawabinsa na sabuwar shekara Gwamna Eno ya bayyana godiyarsa ga Allah da kuma al’ummar jihar bisa goyon bayan da suka ba shi tsawon shekaru biyu da rabi.

“Muna godiya ga Allah Madaukakin Sarki da ya ganmu a cikin wannan shekarar da ta zo karshe don alherinSa ga al’ummarmu da kasarmu da zaman lafiya da muke samu da ci gaban da muka samu tare a cikin shekaru biyu da rabi da suka gabata wanda muka himmatu wajen fadadawa da zurfafa a cikin sabuwar shekara.”

Gwamnan ya kuma yabawa ‘yan jihar Akwa Ibom bisa addu’o’i da hadin kai inda ya yabawa majalisar dokokin jihar bisa amincewa da kasafin kudin na 2026 na karfafawa da fadadawa.

“Wannan ruhun haɗin gwiwar shine dalilin da ya sa mutanenmu suka zabe mu don yin aiki a gare su.”

Ya kuma mika gaisuwar sabuwar shekara ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu inda ya yi alkawarin ci gaba da mara baya ga ajandar sabunta fata.

 

Comments are closed.