Take a fresh look at your lifestyle.

Paparoma Leo Yayi Kira Ga Ci Gaba Da ‘Yancin Venezuela

89

Paparoma Leo na 14 ya yi kira ga Venezuela da ta ci gaba da kasancewa mai cin gashin kanta, ya kuma ce yana bin abubuwan da ke faruwa bayan da Amurka ta hambarar da shugaba Nicolas Maduro da “rai mai cike da damuwa” ranar Lahadi.

Leo, Paparoma na farko na Amurka, ya kuma yi kira da a mutunta ‘yancin ɗan adam da bin doka “kamar yadda aka tanadar” a cikin kundin tsarin mulkin Venezuela.

“Kada mu yi jinkiri wajen shawo kan tashe-tashen hankula da kuma hau kan turbar adalci da zaman lafiya, tare da tabbatar da diyaucin kasar,” Fafaroma ya shaida wa mahajjata a dandalin St. Peter’s a lokacin sallar Lahadi.

Shugaban Amurka Donald Trump a ranar Asabar din da ta gabata ya ce Amurka za ta karbe ikon kasar Venezuela mai arzikin man fetur bayan da ta ba da umarnin kai samame domin cafke Maduro, wanda a halin yanzu yake tsare a wani gidan yari na birnin New York yana jiran tuhume-tuhume kan miyagun kwayoyi.

Leo, wanda ya soki wasu manufofin na hannun daman Trump, a watan Disamba ya bukaci shugaban Amurka da kada ya kori Maduro ta hanyar amfani da karfin soji.

Fafaroman ya ce “Kyakkyawan mutanen Venezuelan da ake kauna dole ne su yi galaba akan duk wani la’akari.”

 

Reuters/Aisha.Yahaya, Lagos

Comments are closed.