Shugaba Tinubu Ya Nada Odusote A Matsayin Shugabar Makarantar Shari’a ta Najeriya
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da nadin Dr Olugbemisola Odusote a matsayin sabon Darakta-Janar na Makarantar Shari’a ta Najeriya.
Nadin ya sanya Dakta Odusote ta zama mace ta farko da ta shugabanci wannan cibiya tun lokacin da aka kafa ta a shekarar 1962.
Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar Mista Bayo Onanuga ya fitar ya bayyana nadin Odusote cewa nadin wanda zai fara aiki daga ranar 10 ga watan Janairun 2026 na tsawon shekaru hudu ne.
Kafin nadinta Dokta Odusote ita ce Mataimakiyar Darakta-Janar kuma Shugabar Harabar Legas zata gaji Farfesa Isa Hayatu Chiroma wanda wa’adinshi zai kare a ranar 9 ga watan Janairun 2026 bayan ya shafe shekaru takwas yana mulki.
Tana da shekaru 54 Odusote tana da fiye da shekaru ashirin na gogewa a cikin tsarin Makarantar Shari’a ta Najeriya. Ta shiga makarantar a shekara ta 2001 a matsayin malama kuma tun daga lokacin ta sami matsayi tana aiki a manyan mukamai da suka hada da Shugabar Sashen Ilimi da Daraktan Ilimi da Shugaban Harabar.
Ta yi digiri na farko a fannin shari’a a Jami’ar Obafemi Awolowo kuma an kira ta zuwa Lauyoyin Najeriya a shekarar 1988.
Daga nan ta samu digiri na biyu a fannin shari’a a jami’ar inda ta kware a fannin shari’a da kasuwanci kafin ta samu digirin digirgir a fannin shari’a a jami’ar Surrey da ke kasar Birtaniya tare da gudanar da bincike kan harkokin shari’a da kuma gudanar da shari’a.
Odusote ta kuma sami ilimin duniya bayan ta yi aiki na ɗan lokaci a matsayin malama mai ziyara a Jami’ar Nottingham Trent da ke Burtaniya.
Karanta kuma: Shugaba Tinubu ya nada Rotimi Oyedepo a matsayin darakta mai kula da kararrakin jama’a
Gudunmawarta na ilimi sun haɗa da wallafe-wallafe da yawa a cikin shahararrun mujallolin dokokin gida da na ƙasa da ƙasa da kuma gabatarwa a manyan tarurrukan ilimin shari’a.
Bayan koyarwa da bincike, ta taka rawar gani a ƙwararrun hukumomin shari’a, tana aiki a cikin kwamitocin Majalisar Ilimin Shari’a da Ƙungiyar Lauyoyin Najeriya.
A matsayin Darakta-Janar Dokta Odusote zata kula da jagoranci a Makarantar ilimin Shari’a ta Najeriya da gudanarwa da dabaru a duk cibiyoyinta.
Za ta kuma kasance babbar hanyar haɗin gwiwa tsakanin cibiyar da manyan masu ruwa da tsaki ciki har da Majalisar Ilimin Shari’a da Ƙungiyar Lauyoyin Najeriya.
Makarantar Shari’a ta Najeriya ita ce hukuma mai zaman kanta da ke da alhakin horar da kwararrun masu neman aikin lauya a kasar.