Uwargidan Shugaban Najeriya Oluremi Tinubu ta yabawa matan gwamnoni da sauran masu ruwa da tsaki kan goyon bayan ofishinta a shekarar 2025.
A cikin sakon da ta fitar a ranar Laraba, Uwargidan shugaban kasar ta ce tallafin da suka bayar a shekarar da ta gabata ya yi yawa.
Mrs Tinubu ta jaddada cewa saboda goyon bayan da suke bayarwa masu karamin karfi a cikin al’umma yanzu suna samun ingantacciyar rayuwa.
KU KARANTA KUMA: Sabuwar Shekara: Uwargidan shugaban kasa ta karrama ‘yan Najeriya
“Yayin da muka shiga sabuwar shekara ina mika sakon godiyata ga uwargidan mataimakin shugaban kasa Hajiya Nana Shettima ko’odinetocin matan shugaban kasa/RHI na jihar matan ‘yan majalisar dokoki ta kasa da matan ministoci da matan shugabannin ma’aikata da sauran shugabannin mata a fadin kasar nan bisa goyon bayan da suka bayar tun farkon wannan gwamnati da kuma ayyukan da muke yi a Reneative Hope.
“Tausayinku sadaukarwarku da shirye-shiryenku sun karfafa kokarinmu na hadin gwiwa wajen isar da ajandar sabunta bege na mai girma shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu GCFR na karfafa dukkan ‘yan Najeriya musamman ma wadanda suka fi kowa rauni ba tare da la’akari da matsayi ko inda aka fito ba” in ji ta.
Uwargidan shugaban kasar ta kuma yi amfani da wannan damar wajen yin kira da a kara sadaukarwa domin ta yi fatan Allah ya karo shekaru masu albarka.
“Har ila yau na yaba da duk kokarinku da hadin gwiwar ku kuma ina fatan ci gaba da goyon bayanku a 2026 da ma bayan haka.
“Ina yi mana fatan zaman lafiya mai albarka da tasiri da wadata a 2026” in ji ta.