Take a fresh look at your lifestyle.

Museveni ya bukaci ‘yan Uganda da su kada kuri’a yayin da zaben ke gabatowa

209

Shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni ya bukaci magoya bayansa da su fito domin kada kuri’a a daidai lokacin da kasar ke shirin gudanar da babban zaben kasar a ranar Alhamis, bayan yakin neman zabensa na karshe a Kampala babban birnin kasar.

 

Dubban mutane ne suka halarci gangamin yawancinsu sanye da rawaya kalar jam’iyyar Museveni mai mulki ta National Resistance Movement (NRM).

 

Shugaban mai shekaru 81, wanda ke kan karagar mulki tun 1986, na neman wa’adi na bakwai a kan karagar mulki.

 

Museveni daya daga cikin shugabannin Afirka da suka fi dadewa kan karagar mulki ya ci gajiyar sauye-sauyen kundin tsarin mulkin kasar da ya kawar da shekarun shugaban kasa da wa’adi.

 

Yunkurinsa na sake tsayawa takara ya zo ne a daidai lokacin da ake sukar gwamnatin kasar kan hakkin dan Adam da murkushe abokan hamayyar siyasa da kuma cin hanci da rashawa.

 

Duk da haka da yawa daga cikin magoya bayansa sun kasance masu aminci. Wani mai goyon bayan NRM Emma Akello ya yaba da shirye-shiryen matasa na Museveni amma ya ce sau da yawa kudaden sun kasa kaiwa ga masu bukata.

 

“Shugaban kasa ya yi wa matasa allurar makudan kudade” in ji ta. “Amma ya kamata mutanen da ke cikin wadannan ofisoshi su nemo hanyoyin da suka dace na isar da wadannan kudade don isa ga matasa musamman ma matasa ‘yan Getto.”

 

Wata mai goyon bayan Gloria Ninsiima ta ce shugabancin Museveni ya fadada damammaki ga mata.

 

Ta ce “Tun lokacin da Museveni ya hau mulki an ceto mu mata.” “An ajiye mu a kicin amma yanzu muna iya magana a bainar jama’a.”

 

A jawabinshi na rufewa Museveni ya yi kira ga magoya bayansa da su kada kuri’a ya kuma yi gargadin cewa “za a murkushe duk wani katsalandan a harkar zaben”

 

An tsaurara matakan tsaro gabanin zaben. Hukumomin kasar Uganda sun girke sojoji da motoci masu sulke a wasu sassan birnin Kampala lamarin da ya janyo damuwa ga ‘yan adawa.

 

Manyan masu kalubalantar Museveni da suka hada da madugun ‘yan adawa kuma fitaccen dan siyasa Bobi Wine sun yi yakin neman zabe. wanda ya tsaya takarar shugabancin kasar a shekarar 2021 ya bayyana a wajen gangamin sanye da hular riga da hula saboda dalilai na tsaro.

 

Ofishin kare hakkin bil adama na Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadin cewa zaben na gudana ne cikin yanayi na danniya da tursasawa inda ya ce an tsare daruruwan magoya bayan ‘yan adawa.

 

Africanews/Ladan Nasidi

Comments are closed.