Take a fresh look at your lifestyle.

Kano: ‘Yan Sanda Sun Hana Shirin Shugo Da Muggan Kwayoyi Da Bama-bamai

95

Rundunar ‘Yan Sanda a Jihar Kano da ke Arewa maso yammacin Najeriya ta samu gagarumar nasara wajen hana aikata laifuka, biyo bayan wani samame da jami’an leken asiri suka yi na dakile yunkurin shugowa da bama-bamai da miyagun kwayoyi a cikin jihar. 

Ayyukan dai sun yi dai dai da umarnin babban sufeton ‘yan sandan kasar Kayode Adeolu Egbetokun kan ingantattun bayanan sirri, jami’an rundunar ‘yan sanda na Rijiyar Lemo da kuma sashin Anti-Daba na rundunar ne suka gudanar da ayyukan. 

A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar CSP Abdullahi Kiyawa ya fitar, rundunar ta ce a farmakin farko na ranar 13 ga watan Janairun 2026, jami’an ‘yan sanda sun aiwatar da umarnin bincike a wani gida da ke Tudun Bojuwa Quarters a karamar hukumar Fag

A yayin binciken an gano wasu manyan buhu biyu dauke da wasu abubuwa da ake zargi da aikata laifuka. 

Kwararru daga Sashen Kashe Bama-Bamai da Sinadarai da Biological da Radiological da Nukiliya (EOD-CBRN) sun yi nazari kan kayayyakin inda suka tabbatar da cewa buhu daya na dauke da igiyoyi masu fashewa guda shida, yayin da buhu na biyu na dauke da buhunan ganye guda 20 da ake zargin cannabis sativa ne da buhu 220 na allunan da ake zargin Exol.

Ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin. A wani samame na daban jami’an rundunar ‘yan sanda ta Anti-Daba da ke aikin leken asiri a lokacin da suke sintiri na sa ido, sun kama wani dan kasuwa mai tuka keke mai uku a unguwar Sani Mainagge da ke karamar hukumar Gwale.

Kiywa ya yi nuni da cewa an gano buhu uku da ake zargin suna dauke da manya-manyan kayan aiki yayin da wasu kwararrun EOD-CBRN suka gudanar da bincike aka gano na’urorin fashewar wutar lantarki guda 3,700.

An kama wani mutum mai suna Ibrahim Garba wanda aka fi sani da “Manyan Baki” mai shekaru 49 daga jihar Zamfara.

Hukumar ta PPRO ta ce wanda ake zargin ya amsa laifin yin jigilar abubuwan fashewa daga jihar Nasarawa zuwa wasu wurare inda ake ci gaba da bincike. 

Kwamishinan ’Yan sandan Jihar CP Ibrahim Adamu Bakori ya yaba wa jami’an da abin ya shafa bisa kwarewa da kuma taka-tsantsan. 

Ya kuma bukaci jama’a da su kasance cikin shiri kuma su gaggauta kai rahoton duk wani motsi, kaya ko wani aiki da suka samu zuwa ofishin ‘yan sanda mafi kusa ko ta lambar gaggawar ‘yan sandan jihar Kano. 

Rundunar ‘yan sandan ta kuma shawarci jama’a da kada su taba duk wani abun da basu da tabbacin sa kuma su nisanta su sannan kuma su sanar da ‘yan sanda nan take.

 

 

Comments are closed.