Take a fresh look at your lifestyle.

Kwankwaso Ya Nuna Aniyarsa Na Komawa Zuwa APC

26

Shugaban jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) na kasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya nuna aniyarsa ta komawa jam’iyyar All Progressives Congress (APC), yana mai cewa irin wannan matakin zai dogara ne da tabbacin da jam’iyya mai mulki ta samu.

Da yake magana a ranar Alhamis da ta gabata a lokacin da yake karbar magoya bayan jam’iyyar NNPP daga kananan hukumomin Rano da Dawakin Tofa a gidansa da ke Kano, tsohon gwamnan ya bayyana cewa bai yanke hukuncin komawa jam’iyyar APC ba amma yana ci gaba da taka-tsan-tsan ne saboda irin abubuwan da ya shafi siyasa a baya.

Kwankwaso ya ce tsarin nasa na da nufin kare magoya bayansa da kuma karfafa matsayar sa na tattaunawa da Shugaba Bola Tinubu da kuma shugabannin jam’iyyar APC.

Ya kuma bayyana cewa an yi kuskuren fahimtar kalamansa dangane da yiwuwar sauya sheka da gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf zai yi.

“Ban taba cewa ba zan koma APC ba,” in ji shi. “Amma kafin daukar wannan matakin, dole ne a ba mu tabbacin makomar gwamnatin jihar Kano.”

Ya nuna damuwarsa kan makomar ‘yan majalisar dokokin jam’iyyar NNPP da magoya bayansa masu biyayya, yana mai jaddada cewa ba zai sauya sheka ba tare da fayyace makomar siyasarsu ba.

“Ba zan tafi APC a makance ba, dole ne in san rawar da nake takawa, da alkiblar tafiya, da kuma abin da zai faru da shirye-shiryenmu na yi wa talakawa hidima,” in ji Kwankwaso.

Da ya ke waiwayi irin kawancen siyasa da suka yi a baya, ya tuna cewa sansanin siyasarsa ya taka rawar gani wajen kawo gwamnatin Muhammadu Buhari amma daga baya aka koma gefe.

Ya ce wannan gogewar ta sanar da dagewar sa kan lamunin kafin kowane sabon daidaitawa.

A cewar Kwankwaso, kawo yanzu babu wani tabbaci ko rubuce-rubuce da aka bayar domin kare muradun tafiyar Kwankwasiyya ko tabbatar da adalci ga ‘ya’yan kungiyar a duk wani sabon tsarin siyasa.

“Ba tare da tabbatattun da rubuce-rubuce ba, barin NNPP zai kasance da wuri kuma yana da haɗari,” in ji shi.

 

Aisha. Yahaya, Lagos

Comments are closed.