Take a fresh look at your lifestyle.

Kotun Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya Ta Amince Da Sake Baben Touadera

150

Kotun tsarin mulkin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a ranar Litinin ta tabbatar da nasarar da shugaba Faustin-Archange Touadera ya samu a zaben shugaban kasar da aka yi ta takaddama a kai a ranar 28 ga watan Disamba wanda ya mika masa wa’adi na uku.

“A madadin al’ummar Afirka ta tsakiya, kotun tsarin mulkin kasar ta ayyana Faustin Archange Touadera a matsayin zababben shugaban kasa a zagayen farko da kashi 77.9% na kuri’un,” in ji shugaban majalisar tsarin mulkin kasar Jean-Pierre Waboe.

Babban abokin hamayyar Touadera, tsohon Firayim Minista Anicet-Georges Dologuele, ya samu kashi 13.5% na kuri’un da aka kada, sakamakon karshe na hukumar zaben ya nuna.

Kotun tsarin mulkin kasar ta ce ta yi watsi da karar da Dologuele ya shigar bayan bayyana sakamakon wucin gadi.

Wani dan takara, tsohon Firayim Minista Henri-Marie Dondra, wanda ya samu kashi 2.97% na kuri’un, a makon da ya gabata ya amince da nasarar Touadera kuma ya ce ya yanke shawarar kin daukaka kara.

“Na yanke wannan shawarar ne domin kiyaye zaman lafiya da kaucewa sake tada rikici. Ina kira ga zababben shugaban kasar da ya dauki matakan da suka dace don sulhunta al’ummar Afirka ta tsakiya da kuma shirya tattaunawa ta gaskiya domin sassauta rikicin siyasa a kasar,” in ji Dondra.

Touadera, mai shekaru 68 masanin lissafin wanda ya karbi mulki shekaru goma da suka wuce, ya yi yakin neman zabensa kan tsaro a kasar da ke fama da rashin kwanciyar hankali.

Reuters/Aisha. Yahaya, Lagos

Comments are closed.