Majiyoyin Syria biyar sun bayyana cewa, Rasha na janye dakarunta daga filin tashi da saukar jiragen sama na arewa maso gabashin kasar Syria, domin kawo karshen dakarunta a wani kusurwar kasar da gwamnatin Damascus ke kokarin karbe iko daga hannun dakarun Kurdawa.
Tun a shekarar 2019 ne Rasha ta girke dakarunta a filin tashi da saukar jiragen sama na Qamishli da ke arewa maso gabashin kasar, wani dan karamin aikewa da aka yi idan aka kwatanta da sansaninta na sama da kuma wani sansanin sojin ruwa a gabar tekun Bahar Rum na Syria, wanda ake sa ran za ta ci gaba da kula da su.
Dakarun gwamnati karkashin shugaba Ahmed al-Sharaa sun kwace yankunan arewaci da gabashin Syria daga hannun dakarun Kurdawa na Syrian Democratic Forces a wannan watan, a daidai lokacin da Damascus ke da burin tabbatar da ikonta a kan daukacin kasar.
An tsawaita wa’adin tsagaita wuta mai rauni a tsakanin bangarorin ranar Asabar har tsawon kwanaki 15. Biyu daga cikin majiyoyin sun ce sojojin Rasha sun fara janyewa a hankali daga filin jirgin saman Qamishli a makon da ya gabata.
Daya daga cikin majiyoyin ya ce ana sa ran wasu daga cikin sojojin za su koma sansanin sojin Rasha na Hmeimim a yammacin Syria yayin da wasu kuma za su koma Rasha.
Wata majiyar tsaron Siriya a gabar tekun yammacin Siriya ta ce an kwashe motocin sojin Rasha da manyan makamai daga Qamishli zuwa filin jirgin saman soja na Hmeimim a cikin kwanaki biyun da suka gabata.
Babu wani karin haske daga ma’aikatar tsaron Rasha. Jaridar Kommersant ta Rasha ta ruwaito a makon da ya gabata, inda ta ambato wata majiyar Syria da ba a bayyana sunanta ba, cewa gwamnatin Syria na iya neman sojojin Rasha da su fice daga sansanin da zarar ta fatattaki Kurdawan saboda “babu wani abin da za su yi (Russia) a can”.
Wani dan jarida ya ga tutocin kasar Rasha har yanzu suna shawagi a filin tashi da saukar jiragen sama na Qamishli a ranar litinin, inda wasu jirage biyu masu dauke da tambarin kasar Rasha suka ajiye akan titin jirgin.
Kasar Rasha, na kusa da hambararren shugaban kasar Syria Bashar al-Assad, ta kulla alaka da Sharaa tun bayan da ya kwace mulki kimanin watanni 14 da suka gabata.
Sharaa ya shaidawa shugaban kasar Rasha Vladimir Putin a shekarar da ta gabata cewa zai mutunta dukkan yarjejeniyoyin da aka kulla a baya tsakanin Damascus da Moscow, alƙawarin da ke nuni da cewa manyan sansanonin soji biyu na Moscow a Siriya suna cikin koshin lafiya.
Reuters/Aisha. Yahaya, Lagos