Shugaban Kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya isa Ankara babban birnin kasar Turkiyya a ziyarar aiki da nufin karfafa alakar da ke tsakanin Najeriya da kasashen Eurasia. Shugaban na Najeriya ya sauka a filin jirgin saman Ankara Esenboğa da misalin karfe 9:05 na dare.
A ranar Litinin din da ta gabata, inda ya samu tarba daga tawagar gwamnatin Turkiyya karkashin jagorancin Ministan Ilimi na kasa Farfesa Yusuf Tekin.
Ana sa ran ziyarar ta Shugaba Tinubu za ta zurfafa hadin gwiwa a tsakanin Najeriya da Turkiyya a fannonin da suka shafi tsaro da ilimi da makamashi da samar da ababen more rayuwa da zirga-zirgar jiragen sama da musayar fasaha.

A yayin ziyarar ta Shugaba Tinubu, kasashen biyu za su shiga tattaunawa ta siyasa da diflomasiyya bisa manyan tsare-tsare kan dabi’un da suka shafi kudi da sadarwa da kasuwanci da kuma zuba jari.
Ajandar za ta hada da ganawa tsakanin manyan jami’an kasashen biyu da kuma rattaba hannu kan yarjejeniyoyin fahimtar juna a bangarori daban-daban da suka hada da binciken kimiyya da makamashi da hadin gwiwar fasaha da kafofin watsa labaru da sadarwa da hadin gwiwar soja da yarjejeniya da dai sauransu.
Ziyarar ta kuma za ta kunshi wani taron kasuwanci da zai hada masu zuba jari daga kasashen biyu domin lalubo hanyoyin da suka dace.

Mambobin tawagar Shugaban Kasar da ke halartar shawarwarin sun hada da Ministan Harkokin Waje, Ambasada Yusuf Tuggar da Babban Lauyan Gwamnati kuma Ministan Shari’a Prince Lateef Fagbemi, SAN da Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (rtd) da kuma Shugaban Kwamitin Tsaro na Majalisar wato Hon. Jimi Benson.
Sauran sun hada da Ministar Harkokin Mata Da Ci Gaban Al’umma, Hajiya Imaan Suleiman-Ibrahim da Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo da Ministar Al’adu da Tattalin Arziki da Kirkire-kirkire, Hannatu Musawa da Mai ba Shugaban Kasa Shawara Kan Harkokin Tsaro, Malam Nuhu Ribadu da kuma Darakta Janar na Hukumar Leken Asiri ta Kasa, Ambasada Mohammed Mohammed.
Ana sa ran Shugaba Tinubu zai dawo kasar a karshen ziyarar.