Shugaban kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya isa Ankara babban birnin kasar Turkiyya a ziyarar aiki da nufin karfafa alakar da ke tsakanin Najeriya da kasashen Eurasia. Shugaban na Najeriya ya sauka a filin jirgin saman Ankara Esenboğa da misalin karfe 9:05 na dare.
A ranar Litinin din da ta gabata, inda ya samu tarba daga tawagar gwamnatin Turkiyya karkashin jagorancin ministan ilimi na kasa Farfesa Yusuf Tekin.
Ana sa ran ziyarar ta shugaba Tinubu za ta zurfafa hadin gwiwa a tsakanin Najeriya da Turkiyya a fannonin da suka shafi tsaro, ilimi, makamashi, samar da ababen more rayuwa, zirga-zirgar jiragen sama, da musayar fasaha.

A yayin ziyarar ta Shugaba Tinubu, kasashen biyu za su shiga tattaunawa ta siyasa da diflomasiyya bisa manyan tsare-tsare kan dabi’un da suka shafi kudi, sadarwa, kasuwanci, da zuba jari.
Ajandar za ta hada da ganawa tsakanin manyan jami’an kasashen biyu, da kuma rattaba hannu kan yarjejeniyoyin fahimtar juna a bangarori daban-daban, da suka hada da binciken kimiyya, makamashi, hadin gwiwar fasaha, kafofin watsa labaru da sadarwa, hadin gwiwar soja, da yarjejeniya da dai sauransu.
Ziyarar da kuma za ta kunshi wani taron kasuwanci da zai hada masu zuba jari daga kasashen biyu domin lalubo hanyoyin da suka dace.

Mambobin tawagar shugaban kasar da ke halartar shawarwarin sun hada da ministan harkokin waje, Ambasada Yusuf Tuggar; Babban Lauyan Gwamnati kuma Ministan Shari’a, Prince Lateef Fagbemi, SAN; Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (rtd); kuma Shugaban Kwamitin Tsaro na Majalisar, Hon. Jimi Benson.
Sauran sun hada da ministar harkokin mata da ci gaban al’umma, Hajiya Imaan Suleiman-Ibrahim; Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo; Ministar Al’adu da Tattalin Arziki Ƙirƙiri, Hannatu Musawa; Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu; da Darakta Janar na Hukumar Leken Asiri ta Kasa, Ambasada Mohammed Mohammed.
Ana sa ran shugaba Tinubu zai dawo kasar a karshen ziyarar.
Aisha. Yahaya, Lagos