Tsohon Darakta a Hukumar Babban Birnin Tarayyar Najeriya (FCTA), Usman Galadima, ya bayyana hadewar Gwamnan Jihar Taraba, Dokta Agbu Kefas da Jam’iyyar APC a matsayin wani mataki da zai kawo karin ayyuka da ribar dimokuradiyya a Jihar.
Da yake zantawa ‘yan jarida, Galadima ya bayyana gwamna Kefas a matsayin shugaba mai wayo kuma jajirtacce wanda ya mai da hankali kan kirkire-kirkire da ci gaban al’ummar jihar Taraba.
A cewarsa, matakin da gwamnan ya dauka na yin aiki kafada da kafada da gwamnatin tarayya ya nuna cewa yana da muradin jama’a a zuciyarsa kuma ya kuduri aniyar jawo karin ci gaba a jihar.
Tsohon daraktan wanda ke da muradin wakiltar mazabar tarayya ta Wukari/Ibi a majalisar wakilai ya bayyana cewa ya yanke shawarar tsayawa takarar ne sakamakon rashin tsarin dimokuradiyyar mazabar.
Ya yi nuni da cewa dole ne wakilan da aka zaba su tafiyar da jama’a a harkokin mulki.
Galadima ya koka da cewa yayin da sauran jihohi ke cin gajiyar ayyukan mazabu, an bar mazabar tarayya ta Wukari/Ibi.
Ya bayyana cewa, saboda kwarewar da ya samu a FCTA da kuma hanyoyin sadarwarsa da aka gina a tsawon shekarun da ya yi yana aiki, yana da kyakkyawan matsayi na kawo sauyi da ci gaba ga mazabar.
Da yake kira ga al’ummar mazabar tarayya ta Wukari/Ibi, Galadima ya bukace su da su mara masa baya, inda ya ba su tabbacin cewa hadin kai zai kawo canjin da ake bukata.
Ya kuma kara da cewa a halin yanzu jama’a na fuskantar kunci duk da cewa yankin na da albarkar noma.
Galadima ya bayyana kwarin gwiwarsa na cewa idan aka zabe shi, mazabar tarayya ta Wukari/Ibi za ta shaida sabuwar alfijir.
Aisha. Yahaya, Lagos