Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS, ta kaddamar da wani shiri na ba da taimakon jin kai a kasar Senegal, domin tallafa wa ‘yan gudun hijira, da marasa galihu, da masu neman mafaka, tare da jaddada aniyarta na tabbatar da mutunta bil’adama, hadin kan yankin da kuma ci gaban kasa baki daya.
Kwamishiniyar raya al’umma ta ECOWAS, Farfesa Fatou Sow Sarr, ta jagoranci wasu manyan jami’an gwamnati, ciki har da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasar Senegal da kuma shugaban kwamitin kula da harkokin ‘yan gudun hijirar da aka dawo da su gida da kuma ‘yan gudun hijira, tare da wakilan hukumar UNHCR, da al’ummomin Casamance da ‘yan gudun hijirar Mauritania a cikin abokan tarayya na ci gaban kogin Senegal.
Shirin, wanda gwamnatin Senegal ta aiwatar ta hanyar kwamitin kula da yanayin ‘yan gudun hijirar da aka dawo da su gida, tare da goyon bayan hukumar UNHCR, wani shiri ne na dala dubu dari biyar wanda zai ba da taimako na ceton rai da tallafawa rayuwa mai dorewa, tare da sauƙaƙa matsa lamba kan al’ummomin da ke karbar bakuncin, inganta zaman lafiya da kuma karfafa zaman lafiya na kasa da kasa
Aisha. Yahaya, Lagos