Shugaban kasa Muhammadu Bhari ya isa jihar Sokoto domin ziyarar aiki na kwana daya.
Shugaban Buhari, wanda ya sauka a filin jirgin sama na Abubakar Sa’ad III na Sokoto da misalin karfe 10:40 agogon GMT, ya samu tarba daga gwamnan jihar, Aminu Tambuwal.
Daga nan ne shugaban zai zarce zuwa fadar mai alfarma Sarkin Musulmi, domin yin mubaya’a ga mai martaba Abubakar Sa’ad III.
Daga baya kuma zai kasance babban bako na musamman a taron shekara-shekara na babban hafsan soji, wanda ake sa ran zai bayyana a bude.
An tsaurara matakan tsaro a ciki da wajen babban birnin jihar a shirye-shiryen ziyarar shugaban na Najeriya.
Mahalarta taron sun hada da manyan hafsoshin sojojin Najeriya.
Ana sa ran taron zai bai wa Jami’an damar yin nazari kan dabarunsu da kuma fito da sabbin dabarun yaki da ta’addanci da sauran kalubalen tsaro.
Shugaba Buhari zai dawo gida Abuja bayan an kamala taron a yau.
Leave a Reply