Jihohi 19 da birnin tarayya zasu amfana da wani shirin inganta Muhalli na “ACReSAL” a najeriya
Kamilu Lawal,Katsina.
Gwamnatin najeriya tayi wani hadin gwiwa da bankin duniya domin inganta muhalli a jihohi sha tara(19) na arewacin kasar da birnin tarayyar Abuja kalkashin wani shiri mai suna “ACReSAL” a takaice
Shirin na “ACReSAL”yana da nufin inganta aikin gona a jihohin domin bunkasar tattalin arzikin kasa
Da yake jawabi a wajen wani taro a birnin Katsina domin karama juna sani tsakanin jami’an da zasu rika bibiyar nasarar shirin a jihohin da zasu amfana, mukaddashin Babban jami’in shirin na Kasa injiniya Ayuba Anda ya bayyana cewa,
“Ana sa ran kashe dalar Amurika sama da miliyan Dari Bakwai ($700,000000) a cikin shekara shidda da za’ayi ana aiwatar da shirin”.
Ya bayyana cewa shirin na da nufin inganta muhalli da kasar noma domin inganta rayuwar al’ummar da shirin zai shafa
“Idan shirin ya samu nasara ana sa ran ya magance matsalar ambaliyar ruwa da sauran matsalolin da sauyin yanayi ke haifarwa domin inganta muhallin da aiyukan gona da nufin inganta tattalin arziki da rayuwar al’ummar da zasu ci moriyar shirin”.
Babban jami’in na “ACReSAL” a najeriya ya kuma bayyana cewa hukumar ta kammala tsare tsaren da suka wajaba domin tabbatar da shirin ya cimma nasarar da ake bukata
“Tsaren tsaren sun hada da amfani da sabbin dabarun noma da inganta muhallin aikin gonar da bunkasa aiyukan hukumomin da zasu tallafama shirin da kuma wani tsari na kulawa domin tabbatar da nasara aiyukan daga farko zuwa kammalawa”.
“Akan haka ne ma muka tattaru a jihar Katsina domin ilmantar da jami’an akan yadda zasu gudanar da aikinsu na tabbatar da samun nasarar shirin a dukkanin jihohin da suka fito”,inji shi.
Leave a Reply