Tsohon Paparoma Benedict na 16 ya mutu a gidansa na Vatican, kusan shekaru goma bayan ya sauka daga karagar mulki saboda rashin lafiya.
Ya jagoranci Cocin Katolika na kasa da shekaru takwas har zuwa 2013, ya zama Paparoma na farko da ya yi murabus tun Gregory XII a shekara ta 1415.
Benedict mai shekaru 95, ya shafe shekarunsa na ƙarshe a gidan sufi na Mater Ecclesiae da ke cikin bangon Vatican.
Magajinsa Paparoma Francis ya ce ya sha kai masa ziyara a can.
A cikin wata sanarwa da fadar Vatican ta fitar ta ce: “Cikin bakin ciki na sanar da ku cewa Paparoma Emeritus, Benedict na 16, ya rasu a yau da karfe 9:34 a gidan ibada na Mater Ecclesiae da ke fadar Vatican.
“Za a ba da ƙarin bayani da wuri-wuri.”
Duk da cewa tsohon Fafaroma ya dade yana jinya, sai dai fadar ta ce yanayin jikin shi yayi tsanani saboda tsufa.
A ranar Laraba ne Paparoma Francis ya yi kira ga masu sauraronsa na karshe a fadar Vatican da su yi addu’a ta musamman ga Paparoma Emeritus Benedict, wanda ya ce ba shi da lafiya sosai.
An haifi Joseph Ratzinger a Jamus, Benedict yana da shekaru 78 a duniya lokacin da a shekara ta 2005 ya zama ɗaya daga cikin manyan fafaroma da aka zaɓa.
A farkon wannan shekara tsohon Fafaroma ya amince da cewa an tabka kura-kurai wajen tafiyar da al’amuran cin zarafi a lokacin da yake babban limamin birnin Munich tsakanin 1977 zuwa 1982.
Leave a Reply