Mai martaba Sarkin Katsina AbdulMumini Kabir Usman ya nada babban darektan hukumar ayyukan sirri ta kasa wato N.I.A., ambasada Ahmad Rufa’i a matsayin sabon sardaunan Katsina
Bikin nadin sarautar ya gudana ne a fadar mai martaba sarkin dake filin Kangiwa a birnin Katsina
Da yake jawabi jim kadan bayan kammala nadin sabon sardaunan, mai martaba AbdulMumini Kabir ya bayyana cewa masarautar tayi la’akari da gudummuwa da aiki tukuru irin na ambasada Ahmad Rufa’i ga cigaban masarautar da jihar Katsina da kasa baki daya a matsayin dalilin bashi sarautar sardaunan
Yana mai bayyana sabon sardunan a matsayin mutum haziki kuma jajirtacce wajen bada gudummuwa ga cigaban al’umma inda ya bukaci al’ummar jihar Katsina da su cigaba da bashi dukkanin goyon bayan da ya dace domin sauke nauyin da aka dora masa
Da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala nada shi,sabon sardaunan na Katsina Ambasada Ahmad Rufa’i ya godema mai martaba AbdulMumini Kabir bisa samun sa a matsayin wanda ya cancanci ya nada matsayin sardaunan, yana mai bayyana aniyar sa ta sauke nauyin da rawanin sardaunan ke dauke dashi
Ya kuma jaddada kudurin sa na cigaba da bada gudummuwarsa ga cigaban al’ummar jihar da najeriya da nahiyar Afrika baki daya
Sarautar Sardauna dai ta samo asali ne daga daular Usmaniya ta Sokoto inda nan ne aka aro ta tare da tuna cewa firimiyan jihar arewa Sir. Ahmadu Bello sardaunan Sokoto mai fimbin tarihi ne akafi tunawa da ita
A masarautar Katsina ma ana bada sarautar Sardauna ga wanda ya kamanta kyawawan halaye irin na marigayi Sir.Ahmadu Bello sardaunan Sokoton wajen bada gudummuwa ga cigaban al’umma a masarautar da jihar da kasa baki daya
A bisa wannan dalili ne massrautar ta Katsina ta baiwa marigayi tsohon sifeton yansandan najeriya,marigayi Ibrahim Ahmadu Commasie sarautar ta Sardaunan Katsina na farko wanda bayan rasuwar sa aka baiwa sanata Ibrahim Ida wanda bayan daga darajarsa zuwa matsayin wazirin Katsina aka samu gurbin sarautar Sardauna
Da samun wannan gurbi ne sai masarautar ta Katsina kalkashin jagorancin Sarki AbdulMumini tayi la’akari da cancantar Ambasada Ahmad Rufa’i aka bashi sarautar tare da yin bikin nada shi a matsayin Sardaunan Katsina na Ukku a wannan rana ta 31 ga watan Disambar 2022.
Bikin nadin na sardauna a fadar mai martaba sarkin na Katsina ya samu halartar manya manyan baki na kusa da na nesa,kamar wakillan shugabannin kasashen Afrika da ministoci da gwamnoni hadi da shugabannin hukumomin gwamnati da kanfanoni da manyan yan kasuwa a ciki da wajen jihar
Daga cikin wadanda suka halarci bikin nadin akwai irin su Ambasada Babagana Kingibe da Ministan ma’aikatar sufurin jirage sama sanata Hadi Sirika da na Shari’a da harkokin kasashen waje watau Abubakar Malami da Geofrey Onyema da sauran takwarorin su
Akwai kuma wakillan sarakuna da masu rike da sarautun gargajiya da gwamnoni da kuma manyan yan kasuwa da jiga jigan kasa irin su Ummaru Mutallab da Alhaji Dahiru Mangal da Dan madamin Daura Alhaji Musa Haro da dai sauran manyan baki
Leave a Reply