Take a fresh look at your lifestyle.

Sabuwar Shekara: Shugaban Cibiyar Kwadago Ya Bayyana Shekarar Ilimin Ma’aikata 2023

Aisha Yahaya, Lagos

0 247

Dangane da rikice-rikicen da ke da alaka da aiki a shekarar 2022, Darakta Janar, Cibiyar NaZarin Harkokin Kwadago ta Michael Imoudu , (MINILS),dake Ilori, Kwanred Issa Aremu, ya sake jaddada aniyar Cibiyar na inganta da zurfafa ingantaccen ilimin kwadago a 2023 don rage yiwuwar hana rikice-rikice a wurin aiki.

 

 

A cikin sakon nasa na sabuwar shekara, Kwamred Aremu ya lura cewa  zaben shugaban kasa da za a yi a watan Fabrairu mai zuwa da cika shekaru 40 da kafa Cibiyar, 2023 ta dauki Najeriya da muhimminci na MINILS bi da bi.

 

 

Ya kara da cewa sabuwar shekara ta nuna shekaru 24 na tsarin dimokuradiyya ba tare da matsalla ba.

 

 

Saboda haka Darakta Janar din ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi amfani da ‘yancinsu na zaben shugaban kasa da ‘yan majalisa da gwamnoni ta hanyar dimokradiyya.

 

 

A cewar shi, “MINILS ta yi farin ciki kuma tana da kwarin gwiwar cewa INEC za ta gudanar da gaskiya da adalci a 2023 tare da inganta harkokin zabukan da suka gabata.

 

 

Kimanin masu kada kuri’a miliyan 90 ne, jam’iyyun siyasa 18 da kuma rumfunan zabe 176,846, Najeriya Zata ci gaba da zama kasa mafi girma a nahiyar Afirka

 

 

Ko da kuwa kalubalen da ake fuskanta a yanzu, Aremu ya lura cewa “Najeriya mai mulkin dimokuradiyya, ta samar da karin ci gaba kuma ta halatta ‘yancin zaben shugabanni.”

 

 

Ya yaba wa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari bisa yadda ya tabbatar da cewa an kirga kuri’u cikin kwanciyar hankali a jihohin Ekiti da Osun kwanan nan,  inda ya kara da cewa “karkashin jagorancin shi na gaskiya da amana, tabbas za ta iya samun sauki ga Najeriya a 2023, tare da sahihin zabe da sakamakon da zai inganta akan shugabanci nagari da cigaba”.

 

 

Kwamared Aremu, ya bayyana cewa Cibiyar Kwadago wacce Marigayi Shehu Shagari ya kafa a shekarar 1983 za ta cika shekaru 40 a shekarar 2023.

 

 

Cibiyar a cewar shi, an shirya ta ne don yin la’akari da aikinta mai inganta aiki da ilimi a cikin shekaru arba’in da suka gabata, ya kara da cewa 2023, ta ba da wani dandamali na jerin ayyukan bikin MINILS a matsayin muhimmiyar ma’aikata ta Afirka,horar da harkokin kasuwanci da kuma  bincike.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *