Take a fresh look at your lifestyle.

PDP Ta Kaddamar Da Gangamin Yakin Neman Zabe A jihar Katsina

KAMILU LAWAL,Katsina.

0 217

Kwamitin gangamin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa da gwamna kalkashin jam’iyyar PDP a jihar Katsina ya kaddamar da taron gangamin sa

 

 

Gangamin wanda ya gudana a karamar hukumar Funtua dake jihar ya samu halartar dan takarar gwamnan Sanata Garba Yakubu Lado da Shugaba da babban darektan kwamitin yakin Neman zaben da shugaban jam’iyyar PDP na jihar hadi da yan takarar kujeru daban daban da dubun dubatar magoya bayan jam’iyyar da dukkanin masu ruwa da tsaki a jam’iyyar ta PDP a jihar Katsina

 

 

Da yake jawabi a wajen taron kaddamar da gangamin, dan takarar gwamnan jihar Katsina a jam’iyyar PDP,Yakubu Lado Danmarke ya bayyana kudurin sa na inganta mahimman bangarorin cigaba domin samar da cigaba mai dorewa a jihar

 

 

 “Idan na samu nasarar zama gwamnan jihar Katsina zan inganta bangaren ilmi da kiwon lafiya da noma da kiwo da ciniki da masana’antu hadi da bangaren tsaro domin inganta rayuwarku da zaman lafiyar ku a fadin jihar nan”, inji Yakubu Lado.

 

 

A nasa jawabin, shugaban Kwamitin yakin neman zaben Sanata Umar Tsauri ya bukaci al’ummar jihar da su fito kwai da kwalkwar su domin zaben yan takarar jam’iyyar PDP a babban zaben na 2023 dake tafe yana mai cewa,

 

 

“Abinda ya rage gareku maza da mata shine kowa yaje gida ya nemi katin zaben sa ya kakkabe shi ya jira lokaci ya zabi jam’iyyar PDP daga sama har kasa a babban  zaben 2023 mai zuwa”.

 

 

Shima a nasa jawabin, babban darektan kwamitin yakin neman zaben na jam’iyyar PDP a jihar Katsina malam Mustapha Muhammad Inuwa yayi Kira ga shugabanni da magoya bayan jam’iyyar su hada kansu domin samun nasarar jam’iyyar, yana mai cewa kwamitin yakin neman zaben zai cigaba da shiga lungu da sako na jihar domin neman goyon bayan al’umma da nufin ganin jam’iyyar PDP ta samu nasara a babban zaben na 2023 dake tafe

 

“Wannan jirgi na kamfen zai ziyarci kananan hikumomi daya bayan daya kuma muna roko ga dukkanin wadanda suke goyon bayan PDP a hadu ai aiki tare Uwa daya Uba daya domin samun nasarar PDP”,inji Mustapha Inuwa.

 

 

Taron Kaddamar gangamin ya kuma samu halartar shugaban matasan jam’iyyar PDP na kasa Muhammad Kadade wanda ya bukaci magoya bayan jam’iyyar da su kama kafa domin kai jam’iyyar PDP ga nasara domin inganta rayuwar su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *