Gwamnatin Najeriya ta saki kudaden fansho N13.89bn domin biyan ma’aikatanta da suka yi ritaya a shekarar 2022.
Hukumar fansho ta kasa ta bayyana haka a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba.
Sanarwar ta ce; “Hukumar fansho ta kasa tana farin cikin sanar da duk masu ruwa da tsaki, musamman ma’aikatu da hukumomin da suka yi ritaya daga asusun ajiya a shekarar 2022 cewa gwamnatin Najeriya ta saki zunzurutun kudi har N13.89bn domin biyan su kudaden fansho da suka tara.
“Hakkin ‘yan fenshon da aka tara yana wakiltar fa’idodin ma’aikaci na shekaru da suka gabata na hidima har zuwa Yuni 2004, lokacin da CPS ta fara aiki.
“Haka zalika, PenCom na sarrafa kudaden da ake aikawa da su a cikin asusun ajiyar kudaden fansho daban-daban na wadanda abin ya shafa, kuma masu gudanar da asusun fansho za su sanar da su nan gaba kadan.
“A karshe, PenCom ya yaba da kokarin mai girma, Mista Shugaban kasa saboda goyon baya da jajircewa wajen aiwatar da CPS da kuma tabbatar da jin dadin wadanda suka yi ritaya.”
Leave a Reply