Ministan cikin gida na Faransa ya bayyana cewa maharin da ya kai hari da wuka ya raunata mutane shida a wani harin ba-zata a tashar jirgin kasa ta Gare du Nord da ke birnin Paris kafin ‘yan sanda su harbe shi.
Mutumin ya kai wa mutane da dama hari, ciki har da dan sanda, da makami mai kaifi da misalin karfe 6:43 na safe (05:43 agogon GMT) kamar yadda Gerald Darmanin ya shaida wa manema labarai a wurin.Ya ce maharin da ba a bayyana sunan shi ba yana tsakanin rai kwakwai mutu kwakwai a wani asibiti.
Fasinjoji da dama da dan sandan kan iyaka na daga cikin wadanda suka jikkata a cewar jami’ai. Maharin ya daba wa jami’in wuka ne a bayansa amma rigar hana harsashi shiga ce ta ceto shi, in ji Darmanin.
Wani daga cikin wadanda harin ya rutsa da su ya samu munanan raunuka a kafadar shi inda aka kai shi Asibiti domin kulawar gaggawa. Darmanin ya godewa ‘yan sanda saboda jajircewa da suka yi. Lamarin ya haifar da tsaikon jirgin kasa a tashar, wacce ke zama cibiyar jiragen kasa zuwa London da Arewacin Turai, da sanyin safiya, a cewar hukumar tashi da saukar jiragen kasa ta SNCF.
Har yanzu dai ba a bayyana dalilin maharin ba. Kasar Faransa na ci gaba da fuskantar tsauraran matakan tsaro bayan wasu munanan hare-haren da aka kai tun shekara ta 2015. A watan Fabrairu ma wani mutum dauke da wuka ya kai hari ga jami’an tsaro a Gare du Nord kuma an kashe shi a nan take.
Leave a Reply