Take a fresh look at your lifestyle.

Manoman Bauchi 16,598 Sun Ci Gajiyar Tallafi

Aisha Yahaya, Lagos

0 149

Kungiyar agaji ta Oxfam a Najeriya ta ce shirinta ya karfafa gwiwar manoma fiye da 16,598 a kananan hukumomi shida na Tafawa Balewa, Alkaleri, Ningi, Darazo, Shira da Gamawa a jihar Bauchi.

 

 

Daraktar kasa ta Najeriya Dr Vincent Ahonsi ne ya bayyana hakan a wajen taron rufewa da koyar da darussan rayuwa da samar da abinci mai gina jiki (LINE) da kungiyar Oxfam tare da hadin gwiwar gwamnatin Canada suka shirya a Abuja.

 

 

 

Ahonsi, wanda ya koka da yadda manoman Bauchi ke fuskantar kalubale da dama a harkokin kasuwancin su, ya ce Oxfam ta dauki matakin ne don ganin ta kawo sauyi a fannin noma a jihar ta hanyar kara kaimi ga kokarin gwamnatin jihar na bunkasa noma.

 

 

 

A cewarsa, “Gwamnatin Canada ta shiga tsakani ne ta hanyar daukar nauyin aikin samar da abinci mai gina jiki (LINE) na dala miliyan 10 wanda Oxfam ta aiwatar a kananan hukumomi shida (LGAs) na jihar Bauchi.”

 

 

 

Ahonsi ya bayyana cewa, an rattaba hannu kan yarjejeniyar aiki tsakanin gwamnatin Canada da Oxfam a ranar 21 ga Maris 2016, kuma an aiwatar da aikin ne a jihar Bauchi.

 

 

 

“Aikin wanda aka kwashe shekaru shida ana gudanarwa ya baiwa kananan manoma 16,598 a kananan hukumomin damar samar da kayan noman rani da suka hada da ciyayi, takin zamani da kuma maganin ciyawa,” inji shi.

 

 

KU KARANTA KUMA: Manoman Bauchi sun yi kira ga FG da ta duba yadda ake noman taki mara inganci

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *