A yunkurin samar da kyakyawar rayuwa ga dakarun sojan Najeriya,Babban hafsan Letana Janar Faruk Yahaya ya kaddamar da aiyyuka a sassa daban daban a jihar Legas.
Aiyyukan da aka kaddamar a ranar 24 ga watan Maris 2022 sun hada da gidan kwana na wucin gadi ga sojojin bangaren kudi da bangaren sufuri har da dkin kwanan dalibai na makarantar horaswa ta soji da kuma karin wasu gidajen kwana ga saje saje daki runduna ta 81,Injiniyoyo da masu bangaren sadarwa.
A jawabin sa daraktan hulda da Jama’a na rundunar Birgediya Janar Onyema Nwachukwu yace hakazalika an gina wa kwamanda da mataimakin shi gidajen kwana a Apapa..Daraktan ya kuma ce wannan rukunin gidajen da aka gina wa sojoji ya nuna cewa an kuduri anniyar kyautata rayuwar dakarun sojin Najeriya .
LADAN NASIDI
Leave a Reply