Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaba Buhari Yayi Alkawarin Goya wa Jihar Osun Baya

0 173

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi alkawarin yin la’akari da bukatun neman taimako da sabon gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, wanda ya kai ziyarar ‘godiya’ a fadar gwamnati a ranar Juma’a.

 

 

 

Gwamnan wanda aka zaba a karkashin tutar jam’iyyar People’s Democratic Party,PDP, ya ce ya yabawa shugaban kasa bisa yadda ya samar da daidaito a zaben da aka gudanar a watan Yulin bara inda ya samu nasara.

 

 

Gwamnan ya ce: “Na yi hakuri da wannan nadin, kuma na yi addu’a sosai a kan hakan. Mafarki

 

 

“Ni ma naci gajiyar sabuwar dokar zabe da kuka sanya wa hannu, domin ta share fagen gudanar da sahihin zabe, tare da kawar da kwace akwatin zabe da cushe.

 

 

 

“Hukumomin tsaro sun bi umarninku na yin adalci da tsayawa, kuma ina alfahari da ku. Kai uba ne na gaske, ba tare da la’akari da bambance-bambancen jam’iyyun siyasa ba,” Adeleke ya shaida wa Shugaban kasar.

 

 

Gwamnan ya ce zaben gaskiya da adalci zai kasance daya daga cikin manya-manyan abubuwan da za’a gada da shugaba Buhari zai bai wa kasar nan, domin kuwa tuni aka fara yabon ci gaban kasar,gida da waje.

 

 

 

Ya sanar da abubuwan da ya sa a gaba a jda suka hada da bunkasa harkar noma, ilimi, da harkar zuba jari.

 

 

 

Daga cikin bukatun da Gwamna Adeleke ya gabatar akwai; tallafi kan samar da ababen more rayuwa, sabon birni na tattalin arziki da yankin ciniki cikin ‘yanci, bashin haraji da sauran cibiyoyin gwamnatin tarayya a jihar Osun.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *