Hukumar kwallon kafa ta Kenya ta dakatar da ‘yan wasa 14 da masu horar da ‘yan wasa 2 saboda gyara wasa bayan ta samu labarin magudi a gasar ta kasa.
Daga cikin wadanda aka dakatar har da ‘yan wasa shida na Zoo Kericho FC, da aka same su da laifin yin gyara a wasa da sashin kula da mutuncin FIFA suka yi a shekarar 2021 tare da kore su daga gasar Premier ta Kenya.
Hukumar ta ce; “Ta dakatar da wadanda ake tuhuma, ciki har da dan wasa daya daga cikin kungiyar Tusker mai mulkin Kenya har sai an gudanar da bincike kan lamarin.”
“Kungiyar Kwallon Kafa ta Kenya ta samu rahotannin sirri da ke zargin ‘yan wasa da jami’ai daban-daban wajen gudanar da ayyukan gyara wasannin,” in ji sanarwar.
Ya ce; “A kokarin kare mutuncin gasar, hukumar ta dakatar da wadannan mutane na wucin gadi har sai an gudanar da bincike kan lamarin daga hukumar FIFA da FKF.”
A watan Fabrairun 2020, FIFA ta dakatar da ‘yan wasan Kenya hudu, daya har tsawon rayuwarsa saboda abin da ya faru a cikin “makircin kasa da kasa” na gyara wasannin gasar.
Daga baya an dakatar da alkalan wasa biyar na Kenya saboda irin wannan badakala.
A watan Nuwamba ne dai Kenya ta dawo fagen wasan kwallon kafa na kasa da kasa bayan da FIFA ta dakatar da ita a watan Fabrairun 2022 saboda katsalandan da gwamnati ta yi a wasan.
Leave a Reply