Take a fresh look at your lifestyle.

Dan Takarar Gwamnan Jihar Neja A Jam’iyyar APC Ya Daga Tutar Fara Kamfen

Aliyu Bello Mohammed, Katsina

0 241

Dan takarar gwamna na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Neja ta arewa ta tsakiyar Najeriya, Umar Mohammed Bago ya kaddamar da yakin neman zabensa tare da yin alkawarin kammala dukkanin ayyukan raya kasa da tsohon gwamnan jihar ya kaddamar a fadin jihar.

Dan takarar gwamna wanda a halin yanzu dan majalisar wakilai ne mai wakiltar ChanChaga a jihar Neja ya bayyana haka a yakin neman zaben shiyyar Sanatan Neja ta Gabas a Kontagora hedkwatar shiyya.

Bago ya ce tsarin gwamnatinsa zai dogara ne kan kara yawan dukiyar jihar ta hanyar gina gadon magabata.

Ya ce gwamnatinsa za ta fi mayar da hankali ne wajen magance tashe-tashen hankulan matasa ta hanyar karfafawa matasa da kuma ingantaccen ilimi domin sanya su cikin al’umma.

A cewar mataimakin shugaban jam’iyyar na shiyyar Arewa ta tsakiya Mu’azu Bawa, magoya bayansa 4,780 ne suka sauya sheka daga wasu jam’iyyun siyasa zuwa jam’iyyar APC mai mulki a Kontagora.

” 87 daga cikin wadanda suka sauya sheka jami’an jam’iyyar PDP ne, mata 261 173 maza daga jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP)”.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *