Take a fresh look at your lifestyle.

Ma’aikatar Albarkatun Ruwa Ta Tarayya Ta Lashi Takobin Wadata Al’uma Da Tsabtataccen Ruwan Sha

Shehu Salmanu, Sokoto

0 286

A babban taron ma’aikatar albarkatun ruwa ta tarayyar Najeriya karo na 29 da ke gudana a birnin Sokoto arewa maso yammacin kasar wanda ya mayar da hankali a kan kuduri na shida na muradu masu dorewa na Majalissar Dinkin Duniya wato Sustainable Development Goals wanda ya mayar da hankali kan samar da ingantaccen ruwan sha ga al’umma da kuma tsabtar muhalli kafin nan da shekara ta 2030.
Tuni dai ministan ma’aikatar Engr. Suleiman Hassan Adamu ya bayar da damar gudanar da taron da nufin kawo karshen matsalolin karancin ruwan sha mai tsabta da kuma tsabatar muhalli.
PIC 1
Taron na kasancewa na hadin gwuiwa da masu ruwa da tsaki a dukkanin harkokin da suka shafi samar da ruwan sha da kuma na amfanin yau da kullum da suka hada da hukumar alkinta ruwa ta NIWRC, Hadeja-Jama’are Water Basin, Sokoto Rima Water Basin inda ake tattauna batun sauyin yanayi, ambaliyar ruwan sama da kuma samar da wutar lantarki ta hanyar ruwan dam ko kogi wanda babbar sakatare a ma’aikar ruwa da albarkatun kasa Uwargida Didi Walson-Jack ta ce zai inganta rayuwar al’ummar Najeriya.
“Ruwa na zaman wani gaggarumi al’amari ga rayuwar al’umma wanda ya sa gwamnatin Najeriya ta maida hankali wajen ganin ta alkinta gami da samar wa al’ummar kasar ruwan sha mai tsabta wanda hakan zai yi dai-dai da muradun da duniya ke kokarin cimmawa nan da yan shekaru masu zuwa.”

A shekara ta 2030 ce ake sa ran cimma wannan kuduri na Majalissar Dinkin Duniya sai dai akwai fargabar idan ba ayi kamar ana yi ba to wankin hula ka iya kaiwa dare kamar yadda kwamishinan ma’aikatar ruwa da albarkatun kasa na jihar Sokoto arewa maso yammacin Najeriya Injiniya Mu’azu Garba wanda kuma shine wakilin gwamnan jihar da ke zama mai masaukin baki ya ce ba zasu yi wasa da al’amarin ruwa a jihar ba.
“Gwamnatin jihar Sokoto kalkashin jagorancin gwamnanta Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal tana iya korinta na wadata al’ummarta da ruwan sha mai tsabta gami da kokarin ganin an ankilta muhalli yadda za a rage yawan kamuwa da cututtukan da ake kamuwa dasu sanadiyar rashin tsabtar muhalli.”

Sai dai wani tarnaki da wannan kokarin ke fuskanta shine rashin ko kuma karancin masu gida rana wato kudi wanda gwamnatoci a matakan jihohi da na tarayya ke fadi tashin ganin sun shawo kan wannan kalubalen .

Abdulkarim Rabiu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *