Kasar Haiti ta fada cikin rashin tabbas na siyasa a ranar Asabar din da ta gabata bayan da majalisar mulkin rikon kwaryar kasar, da ke da alhakin dakile tashe-tashen hankula na kungiyoyi da kuma shirya zabukan da aka dade ana jinkiri, ta kammala wa’adinta ba tare da wani wanda zai gaje shi ba, lamarin da ya bar kasar ta Caribbean ba ta da cikakkiyar ikon gudanar da mulki.
Majalisar rikon kwarya mai mambobi tara (CPT, ta faransanci) an kafa ta ne a watan Afrilun 2024 bayan Firayim Minista Ariel Henry ya yi murabus. An jagorance ta da jerin sunayen shugabannin kansiloli.
Sai dai kuma wa’adin mulkin na shi ya nuna tabarbarewar tsaro, zargin cin hanci da rashawa da kuma fadace-fadacen siyasa.
A karshen watan Janairu, da yawa daga cikin mambobin CPT sun ce suna neman hambarar da Firayim Minista Alix Didier Fils-Aime, duk da cewa Amurka ta yi barazanar mummunan sakamako idan suka yi hakan tare da goyon bayan Fils-Aime ya ci gaba da kasancewa bayan 7 ga Fabrairu.
Amurka ta kuma ce dole ne CPT ta bar mulki kuma ta kakaba takunkumi kan mambobin majalisar biyar.
“Yayin da wa’adin Majalisar Shugabancin rikon kwarya ya kare a ranar 7 ga Fabrairu, muna goyon bayan jagorancin Firayim Minista Fils-Aime wajen gina Haiti mai karfi, wadata da ‘yanci,” in ji ofishin jakadancin Amurka a Haiti ranar Laraba.
Kwana daya kafin nan, jiragen yakin Amurka uku sun isa gabar tekun Port-au-Prince. Ofishin jakadancin ya ce kasancewarsu “yana nuna irin sadaukarwar da Amurka ke yi wajen tabbatar da tsaro, kwanciyar hankali, da kuma kyakkyawar makoma ta Haiti.”
Ko da yake akwai babban yarjejeniya tsakanin shugabannin farar hula da na siyasa na Haiti cewa ya kamata CPT ta sauka, amma har yanzu ba a cimma matsaya kan tsarin da zai maye gurbinta ba.
Da yake magana da jaridar Miami Herald a ranar Laraba da ta gabata, tsohon dan majalisa Antoine Rodon Bien-Aime, wanda ya shiga cikin tattaunawa, ya ce an yi shawarwari da yawa amma har yanzu ba a samu mafita ba.
Kasar Caribbean mafi yawan al’umma ta kasance ba tare da zababben shugaban kasa ba tun bayan kisan Jovenel Moise a 2021, kuma wa’adin Sanatoci na karshe ya kare shekaru uku da suka gabata.
An gudanar da zabe na karshe a shekarar 2016. Yaduwar kungiyoyin masu dauke da makamai a babban birnin kasar Port-au-Prince, da filayen noma na Artibonite da kuma sassan tsakiyar kasar ya kara dagula dabarun shirya zabe na gaskiya da adalci.
Kimanin mutane miliyan 1.4 ne suka rasa matsugunansu a cikin Haiti a watan Oktoba, bisa ga kididdigar Majalisar Dinkin Duniya, miliyan daya fiye da lokacin da CPT ta fara aikinsu.
Majalisar Dinkin Duniya ta kuma amince da wata rundunar tsaro ta kasa da kasa da ke da nufin taimakawa ‘yan sanda wajen dawo da tsaro, amma fiye da shekaru biyu aka tura kasa da sojoji 1,000 – galibi ‘yan sandan Kenya -. Majalisar Dinkin Duniya ta ce tana da burin samun 5,500 a wannan bazarar.
Reuters/Aisha. Yahaya, Lagos