Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika sakon ta’aziyya ga gwamnatoci da al’ummar Turkiyya da Siriya da kuma wadanda suka rasa ‘yan uwa da abokan arziki a girgizar kasar da ta afku a garin Gaziantep da ke kudancin kasar Turkiyya.
Shugaban ya yi wa wadanda suka jikkata fatan samun lafiya cikin gaggawa tare da ba su tabbacin cewa addu’o’i da tunanin ‘yan Nijeriya na tare da su domin tunkarar wannan mummunan bala’i da ya biyo bayansa.
A matsayinsa na aminiyar Turkiyya da Siriya, Shugaba Buhari ya ce Najeriya a shirye take ta ba da cikakken goyon bayan ta ta kowace hanya.
Comments are closed.