Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaba Buhari Ya Murna Da Sabon Shugaban Kwadago, Ajaero

0 124

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya taya Joe Ajaero murnar zama sabon shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya NLC.

 

 

Shugaban ya kuma yabawa kwamitin zartarwa na kungiyar NLC na kasa kan nasarar da majalisar ta samar da sabbin shugabanni.

 

 

“Bayan shekaru masu yawa na aiki tukuru da gwagwarmaya, rashin son kai da Ajaero ya sadaukar da kansa a yau ya biya. Tafiyarsa a cikin ƙungiyar Kwadago ta kasance mai ban mamaki, wanda aka yi masa alama da abubuwa da yawa masu mahimmanci.

 

“Wannan nasarar da ta fito daga majalisa ba tare da tada zaune tsaye ba,”

 

Shugaban ya ce hakan alama ce ta karfin dimokuradiyya a harkar kwadagon kasar.

 

 

Abokin Hulɗa

 

 

“A yau, yayin da ya kai matsayi mafi girma a NLC, fatanmu da burinmu ne ya yi amfani da wannan matsayi wajen rubuta wani sabon babi na ci gaba ga dukkan ma’aikata da kungiyar kwadago a kasar nan da ma Nahiyar baki daya.” Ya bayyana.

 

Shugaban ya kuma bayyana fatan alkhairi ga Ajaero da tawagarsa kuma su ci gaba da ba wa gwamnati hadin kai wajen cimma muradun al’ummar Najeriya.

 

Shugaba Buhari ya kuma taya Kwamared Ayuba Wabba murnar kammala wa’adinsa na shugaban ma’aikatan Najeriya cikin nasara tare da yi masa fatan alheri a cikin ayyukansa na gaba.

 

Ya yi fatan sabuwar hukumar zartaswa ta samu nasara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *