Mambobin tawagar gudanarwar babban bankin Najeriya za su gana a yau Litinin domin duba rikicin da manufar sake fasalin kudin Naira ta haifar domin samar da mafita kan matsalar karancin kudi da ta addabi kasar.
Taron zai kuma yi la’akari da shawarar da Majalisar Dokoki ta kasa ta bayar na cewa babban bankin ya sake buga wasu takardun kudi na Naira 1,000 da N500 da kuma N200 da aka yi wa kwaskwarima ko kuma a sake zagayawa da tsofaffin wadanda aka cire daga kasuwannin domin a samu saukin matsalar kudi da ake fama da ita.
Taron wanda zai gudana a hedikwatar CBN da ke Abuja, zai kunshi manyan jami’an bankin, kuma za a iya fitar da wani sabon umarni ga bankunan Deposit Money kan ko a ci gaba da karbar kudaden da aka ajiye na tsofaffin takardun kudi ko a’a.
Rahotanni sun bayyana cewa, CBN na tunanin ba wa wasu kamfanoni kwangilar buga takardun kudin Naira da aka sake fasalin, amma ya musanta ikirarin cewa yana iya buga sabbin takardun Naira.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar din da ta gabata, mai magana da yawun CBN, Osita Nwasinobi, ya ce babu wani lokaci da gwamnan na CBN ya bayyana haka a lokacin da yake gabatar da shi ga majalisar jiha ta kasa a taronta na ranar Juma’a 10 ga Fabrairu, 2023.
Ya zuwa yanzu dai, hukumar da’ar ma’adanai ta Najeriya ta buga Naira biliyan 500 na sabbin takardun kudi na Naira 1,000 da N500 da kuma N200, yayin da CBN ta cire kusan N2.1tn na tsofaffin kudaden da ake bugawa.
Leave a Reply