Take a fresh look at your lifestyle.

‘Yan Bindiga Sun Kashe Jami’in ‘Yan Sanda Na Shiyya Da Wasu A Jihar Neja

0 202

Rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Neja ta arewa ta tsakiyar Najeriya, ta tabbatar da kashe jami’in ‘yan sandan shiyya (DPO), a yankin Paikoro da wasu ‘yan bindiga suka yi a yayin wata arangama da suka yi da su.

Sanarwar da Kakakin Rundunar, DSP Wasiu Abiodun ya fitar ta ce, DPO, SP Mukhtar Sabiu da wasu jami’an ‘yan sanda 4 sun rasa rayukansu a yayin artabu da bindigar.

Al’amarin a cewar DSP Wasiu ya faru ne lokacin da ‘yan bindigar suka yi yunkurin kai hari a kasuwar kauyen Chibani ta Sarkin-Pawa, a karamar hukumar Munya ta jihar.

“Rundunar ‘yan sanda daga Gawu-Babangida Div. da Paiko Div, sojoji da ’yan banga an shirya su zuwa wurin, kuma ‘yan bindigar sun yi artabu da bindiga tare da fatattakar su tare da kashe da dama daga cikinsu, yayin da wasu suka tsere da raunukan harbin bindiga”.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Neja, CP Ogundele Ayodeji, wanda ya jagoranci tawagar da suka kai harin tare da kwato gawarwakin ma’aikatan da suka mutu, ya jajantawa iyalan wadanda abin ya shafa.

Kwamishinan ‘yan sandan ya kuma tabbatar wa da jama’a cewa rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen yakar ‘yan fashi da sauran miyagun laifuka a jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *