Take a fresh look at your lifestyle.

AFIRKA TA KUDU DOKAR TA BACI SAKAMAKON AMBALIYAR RUWA

0 304

Shugaban Afirka ta kudu Cyril Ramaphosa ya kafa dokar ta baci a kasa sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da ya haifar da ambaliyar ruwa da yayi sanadiyar mutuwar mutane 443 a yankin Durban .

“Majalisar zartaswar tayi taron gaggawa tare da kafa dokar ta baci,” shugaban kasar yace wannan lamari asarar rayukan jama’ a akayi”.

Yau kasar mu na cikin zaman makoki,” Mr Ramaphosa, ya ziyaraci yankin a ranar Laraba.

Tuni aka tura dakaru dubu 10,000 zuwa yankin da bala’ in ya faru domin taimakawa wadanda abun ya shafa  a yankin KwaZulu-Natal (KZN) inda aka samu asarar rayuka mafi muni.

Kamar yadda masu harsashen yanayi suka fada ,cewa  ba za’ a sake samun ambaliyar ruwa ba a cikin kwanaki masu zuwa..

 

LADAN NASIDI

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *