Take a fresh look at your lifestyle.

“Tinubu Zai Gaje Ni” – Shugaba Buhari

0 116

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tabbatarwa ‘yan Najeriya cewa jam’iyyar All Progressives Congress, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu ne zai gaje shi a matsayin shugaban kasar.

 

 

Shugaban wanda ya je Owerri babban birnin jihar Imo a ranar Talatar da ta gabata don taron gangamin shugaban kasa na jam’iyyar APC ya kuma kaddamar da titin MCC da Uratta wani aiki ne da gwamnatin jihar Imo ta kammala kwanan nan.

 

 

Shugaban ya yabawa dimbin magoya bayansa da suka yi dandazo a wurin taron, inda ya ba su tabbacin cewa jam’iyyar APC ba za ta yi nasara a jihar kadai ba, har ma za ta lashe zaben shugaban kasa.

 

Ya ce, “Na zo nan ‘yan uwa da abokan arziki domin na gode muku matuka da kuka nuna kanku na tsawon lokaci don ganin kun karrama Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaban kasarmu na gaba.

 

 

“Babu wani abu da yawa da zan iya cewa shugaban jam’iyyar na kasa da sauran shugabannin jam’iyyar ba su ambata ba. Muna nan a yau, muna matukar godiya da lokacin da kuka fito. Muna matukar godiya da goyon bayanku kuma in Allah ya yarda Asiwaju Tinubu zai kai ga zama shugaban Tarayyar Najeriya. Na gode kwarai da gaske.”

 

 

Tun da farko dai shugaban Najeriya ya yi wata ganawa da majalisar sarakunan gargajiya ta kungiyar, inda ya dora musu alhakin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a yankunan su.

 

Gwamnan jihar, Hope Uzodimma, ya ce jihar Imo ba za ta manta da irin ci gaban da jihar ta samu a gwamnatin shugaba Buhari ba.

 

 

Ya ce, dandazon magoya bayan shi a wajen taron sun yi masa godiya.

 

A cewar Uzodinma: “Mutanen Jihar Imo sun ce in gaya maka cewa ka yi wa al’ummar Jihar alheri. Da muka nemi goyon bayan ku don gina titin Orlu zuwa Owerri kun ba shi.

 

 

“Mun nemi goyon bayan ku don gina titin Okigwe zuwa Owerri kun ba shi. Mun nemi goyon bayan ku don gina titin Owerri zuwa Umuahia kun ba shi. Na zo wurinku na ce ku inganta Cibiyar Kiwon Lafiya ta Owerri zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’a domin dalibai su yi amfani da ita wajen horar da su, kun ba su.

 

 

“Na zo wurinku ne na inganta Kwalejin Ilimi ta Alvan Ikoku zuwa Jami’ar Ilimi ta Tarayya da kuka ba da ita. Lokacin da satar danyen mai ya kusa lalata tattalin arzikin jihar Imo, na nemi a kafa sansanin sojan ruwa a Uguta, kuma ka amince. Shugaba, mutanen Imo suna yaba maka sosai.

 

 

“Kasancewar ka a yau tare da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyarmu babbar shaida ce ta kudurin da kuka yi na ganin jam’iyyarmu ta bunkasa daga inda kuka tashi zuwa babban matsayi na gaske ne.”

 

 

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya yi wa jama’a alkawarin ci gaba da samun ci gaban da ake samu a jihar a karkashin gwamnatin shi.

 

Yace; “A yau na yi muku alkawari, shirin ci gaban APC ba zai tsaya ba. Za mu sanya Jihar Imo ta Zama daya daga cikin mmuhimman wajen yawon bude ido. Za mu ƙara ƙima ga dukiyar ku. Za mu sake ginawa da kyautata hanyoyinku. Za mu zuba jari a fannin ilimi. Ga dukkan ku matasa, karatun jami’a dole ya Zama na shekaru hudu. Babu sauran yajin aikin ASUU.”

 

 

Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdulahi Adamu ya kuma gaya wa dimbin magoya bayan shi suka halarci taron, za a iya cewa jihar Imo ta zama jihar APC a yanzu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *