Ba a ga jami’an tsaro a rumfar zabe mai lamba 1 da kuma 3 na karamar hukumar Oreado da ke jihar Edo a Kudancin Najeriya ba.
Har yanzu ba a fara ba da takardar izini ba a karamar hukumar da ke harabar makarantar firamare ta Ogbe.
Rukunin zaben firamare na Exhorti ya cika makil da masu son kada kuri’a wadanda ke dakon zuwan jami’an INEC.
A halin da ake ciki dai ma’aikacin adhoc 1 ne kawai aka ga suna ta kwaso kayan zabe daga cikin motar bas yayin da jami’an INEC ba su iso ba.
Leave a Reply