Jihar Anambara: Ma’aikatan Hukumar Zabe (INEC) Suna Wajen Zaben Shugaban Kasa Da Na ‘Yan majalisar
Aisha Yahaya, Lagos
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, ma’aikatanta sun cika a mazabar Agulu 2, Anambra Central domin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar tarayya a jihar Anambra a kudu maso gabashin Najeriya.
Tuni aka baje kolin rijistar masu kada kuri’a a rumfar zabe. Wadanda suka cancanci kada kuri’a suma suna tsaye domin fara kada kuri’a a gundumar.
Daya daga cikin dan takarar shugaban kasa Peter Obi na jam’iyyar Labour ana sa ran zai kada kuri’a a gundumar Agulu 2 kasancewar sa na zaben sa.
Sanata Uche Ekwunife na jam’iyyar People’s Democratic Party, Victor Umeh na jam’iyyar Labour da Dozie Nwankwo na All Progressive Grand Alliance ne za su fafata neman tikitin takarar sanatan Anambra ta tsakiya.
Leave a Reply