Take a fresh look at your lifestyle.

Sanatan Kano Ya Yi Alkawarin Tallafin N100m Ga Wadanda Gobara Ya Shafa

12

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Barau Jibrin ya ziyarci Kasuwar singer da ke Jihar Kano domin jajanta wa ’yan kasuwar da wata mummunar gobara ta lalatar da kayayyaki da kadarori na biliyoyin Naira.

A kwanakin baya ne wata gobara ta kone kasuwar da ke karamar hukumar Fagge a Kano, lamarin da ya sanya dubban ‘yan kasuwa ke kirga asara mai yawa.

A yayin ziyarar ta’aziyyar, Sanata Barau ya sanar da bayar da gudunmuwar Naira miliyan 100 domin tallafa wa wadanda abin ya shafa da kuma taimaka musu su fara aikin sake gina sana’o’insu.

Shugaban Kasuwar Singer Alhaji Junaidu Zakari ne ya tarbe shi tare da dimbin ‘yan kasuwar da abin ya shafa da suka taru domin tarbar dan majalisar tarayya.

Da yake jawabi ga wadanda lamarin ya rutsa da su, Sanata Barau ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici ba ga ‘yan kasuwa kadai ba har ma da jihar Kano da Najeriya, inda ya ce har yanzu kasuwanci ne kashin bayan tattalin arzikin jihar.

“Wannan gobara da ta barke da hasarar da aka samu ta shafe mu baki daya, ta shafi daukacin al’ummar Kano da ma kasa baki daya, kasuwanci ce ginshikin Kano, don haka lamarin ya taba mu sosai,” inji shi.

Mataimakin shugaban majalisar dattawan, wanda kuma shine mataimakin shugaban majalisar ECOWAS na farko, ya kara da alkawarin samar da na’urar sarrafa gobara ta zamani a kasuwar domin hana afkuwar lamarin nan gaba.

Shugaban kasuwar, Alhaji Junaidu Zakari, ya bayyana cewa Kasuwar Singer ta fuskanci manyan gobara biyu a ‘yan kwanakin nan, inda aka yi asarar sama da Naira biliyan 5.

Ya godewa Sanata Barau bisa ci gaba da goyon bayansa da kuma daukar matakin gaggawa kan halin da ‘yan kasuwar ke ciki.

“Muna alfahari da samun ku a Kano, muna godiya da irin goyon bayan da kuke ba mu, kun yi mana abubuwa da yawa, mun gode sosai,” in ji shi.

Sanata Barau ya samu rakiyar karamin ministan gidaje da raya birane Yusuf Ata da kodinetan kungiyar Renewed Hope na jihar Kano Malam Salisu Takai da ‘yan majalisar dokokin jihar Kano da sauran mataimaka.

 

Aisha. Yahaya, Lagos

Comments are closed.