Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya kada kuri’arsa a mahaifarsa da ke karamar hukumar Mafa.
Gwamnan ya samu amincewar sa ne a mazabarsa ta Ajari ward, unit no 006 sannan kuma ya kada kuri’arsa da misalin karfe 12:00 na rana.
Gwamnan a wata ‘yar gajeriyar hira da ‘yan jarida bayan ya kammala aikin sa ya shaidawa manema labarai cewa ya gamsu da yadda aka gudanar da aikin kawo yanzu.
“Na gamsu da abin da na gani ya zuwa yanzu, duk da cewa na zo ne ba zan san abin da ke faruwa a wasu rumfunan zabe ba, sai na zagaya don gani da kaina idan ana gudanar da zabe ba tare da wata matsala ba.” Inji Gwamnan.
Gwamna Zulum ya bukaci kowa da ya yi zabe cikin gaskiya kuma ya kamata ya gane cewa Allah ne ke ba da mulki ga wanda ya so.
Tun da farko kafin amincewar gwamnan, jami’an INEC sun shaidawa manema labarai cewa hukumar zabe ta BVAS A-J tana da masu kada kuri’a 863 yayin da BVAS K-Z ke da masu kada kuri’a 809.
Leave a Reply