Take a fresh look at your lifestyle.

A Ranar Litinin Ne Za A Ci Gaba Da Tattara Sakamakon Zaben INEC

0 187

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta dage tattarawa da bayyana sakamakon zaben shugaban kasa na 2023 da karfe 11 na safe a ranar Litinin 27 ga watan Fabrairu.

A ranar Lahadi ne INEC ta bayyana sakamakon zaben shugaban kasa na 2023 na jihar Ekiti da ke kudu maso yammacin Najeriya.

Jami’in tattara sakamakon zaben shugaban kasa na INEC a jihar Ekiti, Farfesa Akeem Olawale Lasisi ne ya fitar da sakamakon zaben 2023 a cibiyar taron kasa da kasa da ke Abuja.

Ya ce Bola Tinubu na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ya samu kuri’u 210,494 sai Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP ya samu kuri’u 89,554.

Peter Obi na jam’iyyar Labour (LP) ya samu kuri’u 11,397 yayin da Rabi’u Kwankwaso na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ya samu kuri’u 264.

Shugaban INEC na kasa, Mahmood Yakubu ya ce hukumar na sa ran sakamakon sauran jihohi 35 da na babban birnin tarayya zuwa ranar Litinin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *