Dan takarar kujerar majalisar dattawa karkashin tutar jamiyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) a yankin Kano ta Kudu ya bukaci jami’an tsaro, hukumar zabe mai zaman kanta INEC da masu sanya idanu na ciki da wajen Najeriya da su mai da hankali kan abubuwan da suke faruwa a wannan yanki.
Hon Kawu Sumaila, ya bayyana haka ne lokacin da yake yiwa manema labarai karin bayani kan batun kona cibiyar tattara sakamakon zabe da aka yi a karamar hukumar Takai dake yankin ya kuma yi sanadiyyar rasa rai tare da jikkata wasu da dama
Tsohon dan majalisar wakilan yayi kira ga jami’an tsaro da su tura tawagar gaggawa zuwa wannan yanki domin kare aukuwar haka a gaba, inda yace “helkwatar tattara sakamako dake karamar hukumar Rano wadda ita ce ke karbar sakamakon mazabar baki daya, ita ce ya kamata a tsaurara matakai a cikin ta.”
Da yake tabbatar da harin, mai magana da yawun rundunar yan sanda ta Kano SP Abdullahi Kiyawa ya ce cikin gaggawa aka kwashe baki dayan kayayyakin zabe, kana kawo yanzu an kama mutane 3 da ake zargi da hannu.
Leave a Reply