Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, ya lashe zaben Sanata mai wakiltar Yobe ta Arewa da gagarumin rinjaye a jihar Yobe.
A daren Lahadi ne hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta ayyana shugaban majalisar dattawa a matsayin wanda ya lashe zaben.
Jami’in zaben ya sanar da cewa, Lawan ya samu kuri’u 91,318, wanda ke wakiltar kashi 74.7 na yawan kuri’u (122,193), inda ya doke abokin takararsa, Bello Ilu na PDP wanda ya samu kuri’u 22,849.
Wannan shi ne karo na bakwai da Lawan ya lashe zaben majalisar a jere tun a shekarar 1999, inda biyun farko suka ba shi tikitin tsayawa takarar majalisar wakilai yayin da biyar na karshe suka ba shi tikitin takarar majalisar dattawa.
Leave a Reply