Gwamnatin Najeriya ta yaba wa tawagar sa ido ta kasa da kasa da aka tura domin gudanar da zabukan shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokokin kasar da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.
Jinjinawar na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Francisca Omayuli a ranar Alhamis.
Ma’aikatar ta ce “tallafin da masu sa ido ke bayarwa ya ba da gudummawa sosai wajen inganta tsarin dimokuradiyya a Najeriya, musamman a zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi masu zuwa.”
Sanarwar ta ce; “Gwamnatin Najeriya na nuna godiya ga al’ummar duniya, kungiyoyin farar hula da sauran abokan ci gaban kasa bisa goyon bayan da suke bayarwa tare da tura tawaga daban-daban na sa ido a Najeriya domin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki.
“Yin zaɓen da aka yi cikin lumana, alama ce da ke nuna yunƙurin Nijeriya na inganta shugabanci nagari da ka’idojin dimokuradiyya. Najeriya ta dogara ne kan ci gaba da fatan kasashen duniya, yayin da gwamnati ke kokarin tabbatar da dimokuradiyya a kasar.
“A kan haka, goyon bayan kowa da kowa zai ba da gudummawa sosai ga ci gaban tsarin dimokuradiyya a Najeriya, musamman yayin da kasar ke shirin gudanar da zaben gwamna da na ‘yan majalisar jiha a ranar 11 ga Maris.”
Leave a Reply