A ranar Litinin dinnan ce rundunar ‘yansanda ta jihar Kano Arewa maso Yammacin Najeriya ta bayyana cewa ta bankado wani shiri da wasu miyagun ‘yan siyasa ke yi na shigo da ‘yan daba don tarwatsa shirin zaben gwamna da za a yi a ranar Asabar mai zuwa.
Kwamishininan ‘yansanda a jihar ta Kano CP Mamman Dauda shi ya bayyana wannan yunkuri ta bakin mai magana da yawun ‘yansandan jihar SP Abdullahi Haruna inda yayi gargadin cewa, duk wani dandaba da ke son kansa da arziki ya kaucewa shigowa jihar da nufin tada hargitsi ko kuma ya fusnkanci hukuncin shari’a.
SP Haruna ya ce rundunar ‘yansandan za ta hada kai da sauran jami’an tsaro don tabbatar da ganin an kama duk wani dandaba da aka samu da laifi don ya gurfana a gaban kuliya.
A cewar kwamishinan ‘yansanda Mamman Dauda rundunar ‘yansanda ta jihar Kano ta samu wasu rahotanni na cewa wasu batagarin ‘yansiyasa na shirin shigo da wasu ‘yandaba daga wajen jihar ta Kano don kawo rudani a zaben gwamna da ‘yanmajalisar jiha da za a yi ranar sha daya ga watan Maris na shekarar 2023.
Kwamishinan yayi gargadi da cewa: “Duk wani batagari da ke da mummunar niyya ga jihar ta Kano ya kaucewa yin hakan don rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen hukunta duk wanda ya taka doka.”
Ya kuma kara da cewa:“ Ina son yin amfani da wannan dama wajen gode wa al’ummar wannan jiha masu bin doka da oda saboda halin dattako da suka nuna a lokacin zaben shugaban kasa da na ‘yanmajalisar jiha. Zaben da ya gudana cikin kwanciyar hankali.”
“Ina fatan al’umma za su ci gaba da ba wa rundunar ‘yansanda hadin kan da ya dace don ganin an yi zabe cikin kwanciyar hankali,” Kamar yadda bayanan na SP Haruna suka nunar.
Leave a Reply