Take a fresh look at your lifestyle.

NLC Ta Zabi Sabbin Shugabanni A Jihar Katsina

Kamilu Lawal,Katsina.

0 127

An zabi Kwamred Hussaini Hamisu Yanduna a matsayin sabon shugaban  Kungiyar kwadago ta kasa(NLC) reshen jihar Katsina a karo na biyu

 

 

An gudanar da zaben ne lokacin  babban taron kungiyar wanda ya gudana a dakin taro na sakatariyar jihar dake birnin Katsina

 

 

Kwamred Hamisu Yanduna ya samu nasarar komawa kujerar sa ba tare da hamayya ba bayan da dukkanin wakillan kungiyar a wajen taron suka amince ya kasance a matsayin sabon shugaban kungiyar reshen jihar Katsina a karo na biyu

 

 

Sauran wadanda aka zaba a matsayin shugabannin kungiyar sun hada da Bishir Amadu a matsayin mataimakin shugaba na daya(I) da Nasiru Wada a matsayin mataimakin shugaba na biyu(II)

 

 

Yayin da aka zabi Haruna Mamman a matsayin Ma’ajin kungiyar sai Zailani Isyaku Kofar Bai da Kabir Gambo a matsayin mai binciken kudi na daya(I) da na biyu

 

 

Sauran wadanda aka zaban sune A’isha Haruna da Hadiza Mamman Danmusa a matsayin Ex-officio ta daya(I) da ta biyu (II)

 

 

A jawabinsa jim kadan bayan jagorantar gudanar da zaben wakilin uwar kungiyar na kasa kwamred Aliyu Ado Minjibir wanda kuma shine mataimakin shugaban kungiyar(NLC) na kasa ya bayyana zaben a matsayin Sahihi kuma amintacce, yana mai kira ga zababbun shugabannin suyi aiki tare domin ciyar da kungiyar gaba

 

 

Shima a nasa jawabin sabon zababben shugaban kungiyar ta NLC a jihar Katsina wanda aka zaba a karo na biyu, kwamred Hussaini Hamisu Yanduna ya godema yayan kungiyar bisa sake zabarshi a karo na biyu tare da basu tabbacin cigaba da aiki tukuru domin ciyar da kungiyar gaba

 

 

Kazalika ya nemi goyon bayan su domin samun nasara a sabon wa’adin da ya karba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *