Shugaban kungiyar kiristoci ta kasa reshin jahar Neja dake arewa ta tsakiyar Najeriya Rev. Bulus Dauwa Yohanna ya yabawa alumma musammam mabiya addinin kirista bisa yadda suka jajirci wajan ganin sun kada kuri’ar su a babban zaben shugaban kasa da na Yan majalisu taraya da ya gudana a karshen watan faberun shekarar nan da muke ciki.
Rev. Bulus Dauwa Yohanna ya Kuma bukaci su da su sake fitowa a zaben gwamna da na yan majalisun jaha da za a yi a mako mai zuwa domin a cewar sa ta haka ne zasu zabe shugabanin na gari da zasu share hawayan su.
” Gaskiya Yana da kyau a duba irin kokarin dan takara da kuma yadda ya gudanar da aikin sa a baya da yadda zai rungumi alumma a nan gaba ta haka ne kadai za a Sami saukin matsalolin da ke addabar alumma. Kowane kirista ya sanin irin hakin dake kansa na zaben Nagari a wannan zaben dake tafe”
Rev. Bulus Dauwa Yohanna ya Kara da cewar ” kungiyar bayan tattauna da shugabanin ta na kasa ta amince a duba batutuwan da suka shafi inganci da mutanta juna da Kuma bin tarihin Dan takarar don ganin irin halin sa da Kuma yadda yake mu’amala da jama’a”
Shugaban kungiyar ya Kuma shawarce su da su Duba chan chanta a lokacin zaben domin kaucewa shiga halin kakanikayi da wasu shugabanin ke jefa alumma da zaran sun kasance kan kujeran Mulki.
Rev. Bulus Dauwa Yohanna ya Kara da cewar akwai bukatar ganin alumma sun bi Chan chanta ga kowane Dan takarar gwamnan da na Yan majalisu ta hanyar Duba irin manufofin su da Kuma abubuwan da suka tsara yiwa alumma da zaran sun Sami nasara a zaben.
Shugaban ya Kuma bukaci alummar kiristoci da su dukufa wajan yin addu’oi da yin azumi tun daga ranakun laraba da alhamis da Kuma jumma’a domin ganin an sami nasarar gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da lumana.
Rev. Bulus Dauwa Yohanna ya ce “kiristoci su zabe duk Wanda suke ganin zai martaba adinai don shine babban abun da yakamata ‘Yan siyasa su Sanya a gaba na ganin ana daraja dukkanin addinai Dake kasar Wanda ta haka ne za a Sami zaman lafiya da kwanciyar hankali a fadin Najeriya”
Leave a Reply