Take a fresh look at your lifestyle.

“Shugaba Buhari Ya Dage Kan Canjin Zaman Lafiya” – COS Gambari

0 108

Shugaban ma’aikatan fadar shugaban Najeriya Farfesa Ibrahim Gambari ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kuduri aniyar ganin an mika mulki cikin lumana.

 

Farfesa Gambari ya bada wannan tabbacin ne a safiyar ranar Asabar jim kadan bayan ya kada kuri’arsa a garin Ilorin da ke jihar Kwara a Arewa ta tsakiya Najeriya.

 

Gambari wanda ya kada kuri’a a mazabar sa mai lamba 004 dake unguwar Akanbi a karamar hukumar Ilorin ta kudu a jihar Kwara, ya bayyana jin dadinsa da yadda zaben ya gudana cikin kwanciyar hankali.

 

Ya kuma yabawa masu kada kuri’a a rumfar zabe bisa yadda suka gudanar da zaben.

 

“Na yi farin ciki, zaben ya gudana cikin kwanciyar hankali, kwanciyar hankali. Ina so in roki jama’ar mu da su gudanar da ayyukansu cikin tsari a duk tsawon lokacin zabe. Daya daga cikin abubuwan gadon da shugaban kasa Muhammadu Buhari yake son ya yi wa Najeriya shi ne gudanar da zabe na gaskiya da adalci.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *