Mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo da uwargidansa Dolapo, sun kada kuri’unsu a zaben gwamnoni da na ‘yan majalisar jiha da aka gudanar ranar Asabar a Najeriya.
Sun kada kuri’a ne da misalin karfe 10:36 na safe agogon Najeriya bayan amincewarsu a rumfar zabe ta 14 da ke Erungege a unguwar Ikenne Ward 1 a karamar hukumar Ikenne a jihar Ogun.
Da yake zantawa da manema labarai, mataimakin shugaban kasa Osinbajo ya bayyana atisayen a matsayin wanda ya yi kyau tare da fatan hakan ya kasance a fadin Najeriya.
Yace; “Ina ganin daga nan, sashin kada kuri’a na, yana da kyau; Ina tsammanin komai yana cikin kwanciyar hankali kuma an gudanar da dukkan tsarin da kyau sosai.
“Ina fata kawai da addu’a cewa ana gudanar da shi a duk fadin kasar, amma ya kasance abin farin ciki sosai.”
“Na yi farin ciki da na samu damar jefa kuri’a kuma da yawa daga cikinmu da ke son kada kuri’u a yau mun samu damar kada kuri’u,” in ji Mataimakin Shugaban.
An fara kada kuri’a a rumfar zabe ta 14 dake Erungege dake unguwar Ikenne 1 da misalin karfe 8:30 na safe agogon Najeriya, kuma komai na tafiya cikin kwanciyar hankali a sashin.
Leave a Reply