Take a fresh look at your lifestyle.

Zaben Gwamn: Jam’iyyun Siyasa Sun Yabawa Hukumar INEC Gaggauci A Enugu

0 294

Wakilan jam’iyyun siyasa a jihar Enugu sun yabawa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC a jihar bisa gaggauwa da suka yi wajen raba kayan zabe.

Sun ce INEC ta yi aiki mai kyau duba da sabanin mummunan yanayin da ya rutsa da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar wakilai inda aka karbi kayan zabe a makare.

Wakilan Jam’iyyar sun tabbatar da cewa an yi ta raba kayan zabe da kuma motsin kayayyakin zabe, tare da cikar jami’an tsaro a ofishin Hukumar rajistar INEC, RAC, da ke Nsukka. Kayayyakin sun isa wasu rumfunan zabe a garin da misalin karfe 8:30 na safe agogon kasar.

Ana gudanar da zabukan gwamnoni da na ‘yan majalisun tarayya ‘cikin tsauraran matakan tsaro da aka sanya domin gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali.

Jami’in zabe mai kula da karamar hukumar Nsukka, Nnenaya Ama ya bukaci mazauna yankin da su kada kuri’unsu cikin hikima domin cin moriyar dimokradiyya.

Ta kuma ba da tabbacin cewa duk wadanda suka cancanci kada kuri’a za su samu damar kada kuri’unsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *