Take a fresh look at your lifestyle.

Zaben HoA 2023: PDP Ta Lashe Mazabar Kaura A Jihar Kaduna

0 183

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), ta bayyana Mista Yusuf Mugu na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben mazabar jihar Kaura da ke jihar Kaduna.

Jami’in da ke kula da zaben ‘yan majalisar jiha a mazabar, Dokta Yusuf Abubakar na Jami’ar Ahmadu Bello Zariya, ya bayyana cewa Mugu ya samu kuri’u 14,085 inda ya doke sauran ‘yan takara hudu.

Ya ce Mista Afan Tandad na jam’iyyar Labour ne ya zo na biyu da kuri’u 12,737, yayin da Mista Sunday Nehemiah na jam’iyyar All Progressive Congress ya zo na uku da kuri’u 8,715. Jami’in zaben ya ce Mista Isaac Gandu na jam’iyyar New Nigerian People’s Party ya zo bayansa da kuri’u 1,121.

Abubakar ya bayyana cewa adadin masu kada kuri’a 37,260 ne aka amince da su daga cikin 101,275 da suka yi rajista a karamar hukumar, inda 37,247 suka kada kuri’unsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *